Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sabon Shugaban Amurka Trump Zai Tsame Hannunwas daga Harkokin Kamfunansa


Donald Trump , shugaban Amurka mai jiran gado
Donald Trump , shugaban Amurka mai jiran gado

Kundun tsarin mulkin Amurka bai yadda shugaban kasa ya hada harkokin kasuwancinsa da gudanar da ayyukan gwamnati dole ne ya bar daya

Shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump yace zai tsame hannunsa baki daya daga kasuwancinsa don gudun sabanin tsakanin kasuwancinsa da shugabancin Amurka idan aka rantsar da shi a ranar 20 ga watan Janairu.

Nan bada dadewa ba zai zama shugaban mafi arziki, Trump ya fada a sakwanninsa na Twitter a jiya Laraba yace zai janye kansa daga kasuwancinsa.

Babu dokar Amurka da ta hana Trump fidda hanayen jarin sa, amma dai yace yana ganin bai dace ba a matsayinsa na shugaban kasa, saboda za a iya samun son zuciya.

Yace aikin shugabancin yana da muhimmanci fiye da duka wani abu.

XS
SM
MD
LG