Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sabon Shugaban Burundi Ya Sha Alwashin Magance Covid-19


Evariste Ndayishimiye, shugaban kasar Burundi
Evariste Ndayishimiye, shugaban kasar Burundi

Sabon shugaban kasar Burundi, Evariste Ndayishimiye ya sha alwashin kirkiro matakan da za a bi domin magance yaduwar coronavirus.

Hakan dai wata sabuwar hanya ce ya dauka daga wanda tsohon shugaban kasar wanda ya gada ya dauka.

Ndayishimiye mai shekaru 52, tsohon soja ne da ya yi ritaya a matsayin janar a rundunar sojin kasar. Ya lashe zaben da aka yi a watan Mayu inda ya kayar da 'yan takara 6.

Shugaba Evariste Ndayishimiye da matarsa Angeline Ndayubaha.
Shugaba Evariste Ndayishimiye da matarsa Angeline Ndayubaha.

A watan Augusta mai zuwa ne ya kamata ya fara aiki amma sai Shugaba Pierre Nkurunziza wanda ke kan kujerar shugaban kasar ya mutu.

Ndayishimiye ya ce gwamnatinsa za ta bayyana sabbin matakan da za a bi a kasar domin takaita yaduwar cutar.

A yanzu dai Burundi na da akalla mutum 170 da suka kamu da Covid-19.

Karkashin Nkurunziza, Burundi ba ta dauki wasu matakan kirki domin magance matsalar Cutar a kasar ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG