Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sabon Shugaban ECWA Na Takaicin Yawaitar Gwauraye Da Marayu Sanadiyar Ta’addanci


Kaddamar da sabon gidan talibijan na ECWA a Jos
Kaddamar da sabon gidan talibijan na ECWA a Jos

Darikar ECWA mai hedkwata a Jos babban Birnin jihar Filato ta rantsar da sabbin shugabanninta tare da kaddamar da gidan talibijan da zai taimaka da shirye-shiryen wanzar da zaman lafiya

Darikar ECWA Ta rantsar da sabbin shugabanninta da zasu ja ragamar ayyukan cocin.

Sabon shugaban darikar Rabarand Stephen Panyam Baba ya bayyana rashin jin dadinsa da yawaitar gwauraye da marayu a Najeriya sabili da ayyukan ta’addanci.

Sabon shugaban ya bayyana cewa darikar ECWA za ta ci gaba da bisharar hadin kan al’umma musamman a sabon gidan talibijan da ta bude.

Ya ce sun gane cewa a duniya yau ana yin wa’azim da ban a Ubangiji ba. Yace suna adu’ar ganin wa’azin Gaskiya ya bazu a duniya duka”.

Dangane da abubuwan da jama’a zasu gani a talibijan din Rabarand Stephen Panyam Baba y ace zasu ga abubuwa iri-iri da suka hada da bishara domin su san yadda zasu samu ceto. Akwai kuma shirye shiryen da zasu taimaka da rayuwa a wannan duniyar musamman matasa akan yadda zasu yianfani da iliminsu da kuma hannayensu.

Akan inganta zaman lafiya Rabarand Baba y ace akwai shirye-shiryen da zasu koyawa Kiristoci yadda zasu zauna lafiya su kuma kawo zaman lafiya tare da hadin kai domin a ci gaba.

Shi ko tsohon shugaban darikar wanda ya sauka Rabarand Jeremiah Gado ya yabawa ‘yan ECWA saboda goyon baya da suka bashi. Ya kara da jaddada batun kaunar juna. Yana cewa “ Wannan gidan radiyo da talibijan zasu yi batun kauna. Babban abu cikin dokoki duka, Yesu ya ce mu kaunaci Allah mu kaunaci juna, shi ne shirye shiryen da wannan talibijan zai rika gabatarwa. Ba na kiyayya ba, amma na hada kan mutane. Yace mun kaunaci ‘yan uwanmu kamar yadda muka kaunaci kanmu. Gidan talibijan din zai gabatar da shirye shiryen zumnci da salama domin mu zo mu tuba a gaban Allah”

A karshe Rabarand Gado y ace duk wanda yake da tsoro da kaunar Allah ba zai yiwa dan’uwansa mugunta ba sai dai ya yi masa Alheri.

Shi ko kwamishanan yada labarai na jihar Filato Yakubu Datti wanda ya wakilci gwamnan jihar a taron ya bayyana goyon bayan gwamnati ga kungiyoyin addini dake shirye-shirye masu kyau. Y ace jihar ta dade tana fama da rikici amma idan an samu kungoyin addini suna yada labaran haddin kai, gwamnati za ta rungumesu.

A saurari rahoton Zainab Babaji da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:19 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG