Accessibility links

Sabon Shugaban Faransa Ya Gana Da Shugabar Jamus Angela Merkel

  • Aliyu Imam

Sabon shugaban Faransa Francois Hollande daga hagu, takwarar aikinsa ta Jamus Angela Merkel daga hanun dama, a taro da manema labarai a Jamus.

Shugabar Jamus Angela Merkel da sabon shugaban Faransa Francois Hollande sun nemi daidaito kan hanyoyin warware matsalolin tattalin arziki dake addabar Turai a ganawarsu ta farko.

Sa’oi bayan rantsar da shi a matsayin sabon shugaban kasar Faransa, Mr. Hollande ya tashi zuwa birnin Berlin domin tattaunawa da shugabar gwamnatin kasar Jamus Angela Merkel

wajen wani taron manema labarai na hadin guiwa, Ms. Merkel tace tana fata kasar Girka wadda bashi ya dabaibaye, zata ci gaba da kasancewa membar kungiyar kasashe masu amfani da takardar kudin Yuro, wani burin da shi ma Mr. Hollande ya jaddada. Dukkan shugabannin biyu sun kuma bayyana bukatar ganin an tsara shirin habakar tattalin arziki yayinda ake aiwatar da tsarin tsuke bakin aljihu a kasashen 17 masu amfani da takardar kudin Yuro, yadda zasu iya fitowa daga mummunar koma-bayan tattalin arziki da matsanancin karancin kudin da suke fama da su.

Sai dai wannan alamar hadin kan da suka nuna, ba ta warware manyan bambance-bambancen ra’ayin dake tsakanin shugabannin biyu ba.

Shugaba Hollande yace hakkinshi shine na aikewa da sako ga kasar Girka, kuma yayi na’am da cewa ya san mawuyacin halin tattalin arzikin da kasar ke ciki. Jam’iyyun siyasa masu yin adawa da shirin tsuke bakin aljihu a fili, sun samu tasirin fada-a-ji yanzu haka a siyasar kasar, abinda ke janyo damuwa a kan ko kasar zata yi aiki da alkawarin da ta yi na aiwatar da sharudan yarjejeniyar ba kasar tallafin kudi da kuma makomarta a kungiyar kasashe masu amfani da takardar kudin Yuro. Waziriya Merkel ita ce ta jagoranci bullo da yarjejeniyar kasafta kudi ta kasashen Turai, wadda ta bukaci kasashen da suka sa hannu, su daidaita kasafin kudin kasashensu.

An rantsar da Mr. Hollande a matsayin sabon shugaban kasar Faransa ‘yan sa’oi kafin ganawar shugabannin biyu. Yace yana so ya sake tattaunawa a kan wannan yarjejeniyar kasafta kudi ta kasashen Turai, domin shigar da shirye-shiryen habaka tattalin arziki a wani bangare na tsamo kasashen daga cikin matsalar da suka fada.

Shugabar gwamnatin kasar Jamus Merkel tace, babu abinda za a sauya a cikin wannan yarjejeniya da aka rattabawa hannu a shekarar da ta shige, aka kuma cimma tare da hadin kai da goyon bayan tsohon shugaban Faransa, Nicolas Sarkozy.

Amma kuma Mr. Hollande ya nemi kawar da irin muhimmancin da ake dorawa a kan bambance-bambancen ra’ayinsu. Yace ganawar aikinsa ta farko da Ms. Merkel ta gabatarwa tare da neman sanin juna ne, kuma lokaci ne na hada kai wuri guda domin samo hanyoyin warware matsalolin tattalin arzikin nahiyar Turai. Ms. Merkel ta ce ta yarda da wannan ra’ayi da ya bayyana.

XS
SM
MD
LG