An zabi Sanata Ahmad Lawan a matsayin sabon shugaban Majalisar Dattawan Najeriya yayin da aka kaddamar da sabuwar majalisa a juko na tara.
Sanata Lawan ya kasance zabin Shugaba Muhammadu Buhari da kuma jam’iyyarsa ta APC.
Wakiliyar Muryar Amurka da ke majalisar, Medina Dauda, ta ruwaito cewa Lawan ya samu kuri’u 79 yayin da abokin hamayyarsa, Sanata Ali Ndume ya samu kuri’u 28.
Ita dai jam’iyyar adawa ta PDP ta marawa Ndume baya ne domin yin hannun riga da zabin APC da Buhari.
Ndume ma dan jam'iyyar APC ne.
Bayanai sun yi nuni da cewa, zababben Sanata Yahaya Abdullahi ne ya fara gabatar da bukatar a zabi Lawan, inda ya samu goyon bayan Sanata Adeola Olamilekan.
A lokacin hada wannan rahoto, ana kan zaben mataimakin shugaban majalisar ta Dattawa yayin da idan an kammala za a yi zaben Kakakin majalisar wakilai.
Za ku iya son wannan ma
-
Fabrairu 03, 2023
'Yan Kasashen Waje Masu Saka Ido A Zabe Sun Fara Isowa Najeriya
-
Fabrairu 03, 2023
Kotu Ta Raba Auren Diyar Ganduje
-
Fabrairu 03, 2023
Wani Bene Mai Hawa Uku Ya Rushe a Abuja
-
Fabrairu 02, 2023
Al'ummar Najeriya Sun Shigar Da Karar Kamfanin Shell A Kotu A Landan