Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sabon Babban Shugaban Muryar Amurka Ya Kori Wasu Jiga-jigan Hukumar


Michael Pack, sabon shugaban USAGM

Sabon shugaban hukumar rukunin kafafen yada labarai na kasa da kasa mallakin gwamnatin Amurka (USAGM) wacce Muryar Amurka ke karkashinta, ya kori wasu shugabannin kamfanonin hukumar.Mic

Michael Pack ya bayyana matakin ne a cikin wata sanarwa da ya fitar da yammacin jiya Laraba.

Kamfanin dillancin labarai na AP ya ce Pack bai bayar da dalilin korar nasu ba, illa kawai ya jaddada cewa ya na aikinsa ne a matsayin shugaban hukumar.

A cikin wadanda ya kora akwai shugabannin Radio Free Asia da kuma Radio Free Europe/Free Liberty wadanda duk su ke karkashin hukumar ta USAGM.

A ranar Litinin din da ta gabata ne shugabar Muryar Amurka Amanda Bennet da mataimakiyarta Sandy Sugawara suka yi murabus.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG