Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sabon shugaban Zimbabwe ya koma kasar jiya Laraba


Emmerson Mnangagwa, sabon shugaban Zimbabwe mai jiran gado da za'a rantsar gobe Juma'a
Emmerson Mnangagwa, sabon shugaban Zimbabwe mai jiran gado da za'a rantsar gobe Juma'a

Mr. Emmerson Mnangagwa wanda shi ne mataimakin shugaban kasa kafin shugaba amaugabe ya tsigeshi abun da ya sa yayi gudun hijira, jiya ya koma kasar a matsayin sabon shugaban kasa biyo bayan matsin lambar da aka yiwa tsohon shugaban har yayi murabus

Shugaban Zimbabwe mai jiran gado Emmerson Mnangagwa ya dawo kasar jiya Laraba bayan ya shafe kimanin makwanni biyu ya na gudun hijira a kasar waje. Dawowar sa ya biyo bayan murabus din dadadden Shugaban kasa Robert Mugabe ranar Talata.

Kakakin Majalisar Dokokin Zimbabwe y ace za a rantsa da Mnangagwa a matsayin sabon shugaban kasa a gobe Jumma’a. Mnangagwa, wanda shi ne tsohon Mataimakin Shugaban kasar, ya gudu daga kasar, haka kwatsam bayan da Shugaba ya kore shi.

Wani babban jami’i a Cibiyar Hulda da Kasashen Waje na Amurka John Campbell, yace ganin yadda Mnangagwa ya taka muhimmiyar a gwamnatin Mugaba, bai tsammanin za a ga wani canjin kirki a salon gwamnati cikin wani kankanin lokaci.

Mugabe, dan shekaru 93 da haihuwa, ya shugabanci Zimbabwe tun daga lokacin da kasar ta zamu ‘yancin kai daga Burtaniya a 1980.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG