Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sabon Tallafi Na Rayuwa Ga ‘Yan Venezuela


Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Linda Thomas-Greenfield ta yi shelar ware kusan dala miliyan 407 na wani sabon tallafi na jin kai ga mutanen Venezuela.

Tallafin ga mutanen Venezuela da ke wahala sakamakon matsalar tattalin arzikin da gwamnatin Maduro da 'yan barandanta su ka haddasa, wanda ya gurgunta tattalin arzikin Venezuela, ya kuma tilasta miliyoyin ‘yan kasarta gudu daga ƙasarsu, kuma sun bar wasu miliyoyin a cikin Venezuela suna buƙatar taimakon agaji.

Ta bayyana hakan ne a tsakiyar watan Yuni yayin babban taro ta kafar yanar gizo na masu ba da gudummawa na kasa da kasa don nuna goyon baya ga 'Yan Gudun Hijira na Venezuela.

A tsawon rabin karni na ashirin, kasar Venezuela mai arzikin mai ta kasance daya daga cikin kasashen Latin Amurka masu matukar arziki, tana alfahari da daya daga cikin kasashe masu karfin tattalin arziki a Latin Amurka.

Amma a cikin shekaru goma da suka gabata ko makamancin haka, saboda rashin shugabanci da rashawa na gwamnatin Nicolás Maduro, Venezuela ta fada cikin rikicin tattalin arziki. A yau, daya daga cikin ‘yan kasar ta Venezuela uku suna cikin matsalar rashin abinci, tsarin lafiya ya kusa durkushewa, kuma babu wani karshen hango wahalar jin kai na mutanen Venezuela. Don haka, 'yan Venezuela sun gudu daga ƙasar cikin rukuni. Tun daga shekara ta 2015, sama da miliyan 5.6 daga cikin mutanen kusan miliyan 30 sun tsere daga ƙasar.

Sabbin kudaden da aka sanar za su taimaka wajen tallafa wa wadannan ‘yan kasar ta Venezuela da suka tsere zuwa kasashe 17 a duk fadin Latin Amurka, da kuma al’ummar da ke karbar su. Hakanan zai kai ga taimaka wa 'yan Venezuela miliyan 7 da ke zaune a cikin Venezuela kuma suka tsinci kansu cikin tsananin bukatar taimako.

"Wannan sabon tallafin kudin zai samar wa mutanen Venezuela dinbin ayyuka na ceton rayuwa da mahimmiyar taimako, kamar abinci, kiwon lafiya, tsaftataccen ruwan sha, matsuguni na gaggawa, samun sukunin hidimar shari'a da kariya, da kuma hanyoyin samun rayuwa," in ji Ambasada Thomas-Greenfield.

Tallafin zai samar da kariya ga kungiyoyin masu rauni wadanda suka hada da mata, matasa LGBTQI +, da kuma 'yan asalin kasar, da kuma taimako na musamman a yayin annobar COVID-19.

“A yau, na sake tabbatar da kudurin Amurka na taimaka wa Venezuela,‘yan gudun hijira da bakin haure, al’ummomin da ke karbar bakuncin da ke tallafa masu, da kuma wadanda suka fi kowa rauni har yanzu a Venezuela wadanda ke fuskantar wani mummunan yanayi, hadadden rikicin jin kai. Na kuma sake tabbatar da kudurinmu na magance matsalar ta hanyar lumana, ta hanyar siyasa, ”in ji Ambasada Thomas-Greenfield.

"Amurka na ci gaba da tsayawa tsayin daka kan goyon bayanmu ga jama'ar Venezuela a gwagwarmayar da suke yi na maido da dimokiradiyya da bin doka da oda."

XS
SM
MD
LG