Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sai Da Muka Biya Naira Miliyan 75, Babura 5 Kafin A Sako Yaranmu - Iyayen Yaran Tegina


‘Yan bindiga.
‘Yan bindiga.

‘Yan bindigan da suka yi awun gaba da yaran islamiyyar ta garin Tegina dai sun rike yara a tsawon kwanaki 88 kafin suka sako su da maraicen jiya Alhamis.

Wasu daga cikin iyayen yaran makarantar Islamiyyar Salihu Tanko dake garin Tegina a jihar Naija sun tabbatar da biyan akalla naira milyan 75 da babura 5 sannan aka sako ‘ya’yan su.

Iyayen wadanda suka bukaci a sakaya sunan su, sun tabbatar da hakan ne ga wakilin Muryar Amurka ta wayar tarho.

Baya ga kudin fansa da babura 5 da iyayen suka tattarawa yan bindigar, sai da kuma suka yi ta tura katin wayar salula na kimanin naira dubu biyar-biyar kusan kullum ga yan bindigar, kamar yadda wata uwa mai ya’ya biyu a cikin yaran da aka sako din ta shaidawa wakilinmu.

‘Yan bindigar da suka yi awon gaba da yaran islamiyyar ta garin Tegina dai sun rike yara a tsawon kwanaki 88 kafin su sako su da yammacin jiya Alhamis.

Bayan sace yaran su sama da 100 a ranar 30 ga Mayun shekarar 2021, kusan kullum ana samun labarin iyayen yaran na neman gwamnati da sauran al’umma cikin hawaye a garin na Tegina da su kubutar mu su da ‘ya'yansu biyo bayan yadda yan bindigar suka ki sako yaran da su ke garkuwa da su bayan sun karbi kudin fansa na naira miliyan 50 da iyayen suka tattara suka bayar da farko.

A baya rahotanni sun yi nuni da cewa 17 daga cikin yaran 136 da ke hannun yan bindigan sun sami arcewa daga dajin da aka ajiye su tare da rahotannin wasu 6 daga cikinsu kuma sun rasa ransu a cikin daji.

Haka kuma, da farko yan bindigar sun amince za su sako sauran yaran 116 idan iyayen daliban sun biya kudin fansa na naira miliyan 50 bayan da batagarin suka rage kudin fansan daga naira miliyan 200.

An sami damar tattara naira miliyan 30 tare da kai kudin wani wuri da aka amince da su yan bindigan a cikin daji, baya ga biyan naira miliyan 20 da aka bayar a watan Yuni.

Yadda Daliban Da Aka Sako A Najeriya Suka Hadu Da Iyayensu Cikin Yanayi Mai Sosa Rai

Yadda Daliban Da Aka Sako A Najeriya Suka Hadu Da Iyayensu Cikin Yanayi Mai Sosa Rai
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:33 0:00

Saidai bayan kirga kudin da yan bindigar suka yi kamar yadda rahotanni suka bayyana, masu garkuwa da yaran sun bayyana cewa kudin bai cika ba saura naira miliyan 4 da dubu 600 inda kuma suka rike wanda ya kai kudin fansar, yayin da su ka ci gaba da rike daliban.

Daga baya yan bindigar sun kira wasu daga cikin iyayen yaran ta waya suna neman sauran naira miliyan 4 da dubu 600 tare da ragowar wasu naira miliyan biyu daga cikin naira miliyan 20.

Daga bisani kuma yan bindigan sun nemi karin kudin fansa da babura kirar Bajaj guda 6 daga hannun iyayen kafin su sako yaran islamiyyar.

Shugaban makarantar Islamiyyar ma, Alhaji Garba Alhassan ya tabbatar da sakin daliban makarantar na Salihu Tanko dake garin Tegina, inda ya ce an sake su ne a kusa da kauyen Birnin Gwari na jihar Kaduna.

Tuni dai yan Najeriya daga ciki da wajen kasar musamman wadanda suka yi kokarin kai gudumuwa ga iyayen daliban suka yi ta murna da godiya ga ubangiji da sako daliban.

Hauwa Mustapha Babura na daga cikin wadanda suka yi gwagwarmayyar neman a sako daliban a kafar Instagram, inda kusan kullum ta ke sako faifan bidiyo na neman gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki su taimaka wajen kubutar da yaran na makarantar Islamiyyar Salihu Tanko har ya kai ga kirkiro shafin murdar Arewa a Instagram inda ake neman mafita ga matsalolin tsaro da ake ciki musamman a arewacin Najeriya.

XS
SM
MD
LG