Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sai Tayu Gadhafi Ya Jikkata Daga Hare haren NATO


Photo shugaban Libya Moammar Gadhafi.

Ministan harkokin wajen kasar Italiya Franco Frattini, yace an sami rahotannin da ba’a tabbatar dasu ba dake cewa mai yiwuwa ne shugaba Moammar Gadhafi ya jikkata sosai

Ministan harkokin wajen kasar Italiya Franco Frattini, yace an sami rahotannin da ba’a tabbatar dasu ba dake cewa mai yiwuwa ne shugaba Moammar Gadhafi ya jikkata sosai a dalilin hare-haren jiragen saman yakin da NATO data shafe makonni tana kaiwa a Libya.

A yau Juma’a minista Frattini yake shaidawa taron manema labarai cewar ya sami rahotan ne daga wajen wani babban limamin Katolika dake zaune a Tripolin Libya cewa saboda tsananin jikkatar da Gadhfin yayi, cikin asiri ya fice daga birnin Tripoli.

Amma wani jami’in Gwamnatin Libya ya musanta wannan rahoto, yace karya ce tsagwaronta.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG