Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sakamakon farko na zaben raba gardama a Sudan na nuni da cewa akasarin al'ummar yankin sun zabi ballewa daga arewaci

Ma'aikatan hukumar zaben raba gardama a kudancin Sudan, 16 Jan 2011
Ma'aikatan hukumar zaben raba gardama a kudancin Sudan, 16 Jan 2011

Sakamakon farko na zaben raba gardama a Sudan na nuni da cewa akasarin al'ummar yankin sun zabi ballewa daga arewaci

Sakamakon farko na zaben raba gardama na nune da cewa akasarin ‘yan Kudancin Sudan sun zabi ballewa daga Arewaci. Jami’an gwamnatin Sudan sun ce za su mutunta wannan zabin kuma a yanzu hankalinsu ya karkata ne kan yadda za a raba kasa mafi girma a Afirka, ciki har da batun rubuta sabon kundin tsarin mulki da kuma fayyace makomar yankin kasar mai arzikin man fetur da ake takaddama akai. Ibrahim Ghandour, wanda shi ne shugaban sashen harkokin siyasa na jam’iyyar da ke muliki da ke da ofis a Khartun ya bayyana cewa, gwamnatin kasar zata mutunta zabin kudancin.

XS
SM
MD
LG