Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yawan Masu Kada Kuri’a a Kudancin Sudan Zai Kai 60%


Wata gyatuma 'yar Kudancin Sudan na kada kuri'arta

Masu shirya zaben raba gardama game da batun ‘yancin kan Kudancin Sudan sun ce yawan masu kada kuri’a zai kai 60% wanda zai bada hurumin halatta dukkannin kuri’un da aka kada a zaben raba gardaman da aka gudanar game da makomar yankin

Masu shirya zaben raba gardama game da batun ‘yancin kan Kudancin Sudan sun ce yawan masu kada kuri’a zai kai 60% wanda zai bada hurumin halatta dukkannin kuri’un da aka kada a zaben raba gardaman da aka gudanar game da makomar yankin.

Wani jami’in hukumar zaben, Su’ad Ibrahim Eissa, ya fadi a wani jawabi yau Laraba cewa yawan wadanda su ka fito zai ma zarce a kalla 60% din da ake bukata.

Saidai an san cewa mutane kusan miliyan 4 aka yi wa rajistar jefa kuri’unsu a wannan zaben raba gardaman da ake da karfin gwiwar zaton cewa zai kai ga yankin na Kudanci Sudan ya balle daga Sudan, ya zama Kasa mai cin gashin kanta

Majalisar Dinkin Duniya ta ce ana sa ran samin sakamakon wacin gadi zuwa ran 2 ga watan gobe, inda kuma takamaiman sakamako zai samu cikin sati biyu na biye.

Akasarin zaben dai an yi shi ne cikin kwanciyar hankali, kodayake an yi ta samin muggan fadace-fadace tsakanin kabilun da ke daura da kan iyakokin Arewa da Kudu a Gundumar Abyei da ake rikici a akai.

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG