An kamala tantance jimlar kuri’un da kowanne dan takara ya samu a zaben fidda gwani na jam’iyyar Adawa ta APC.
‘Yan takarar sune tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, gwamnan Jihar Kano Rabiu Musa Kwankwaso, gwamnan Imo Rochas Okorocha, tsohon shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari da shugaban kamfanin jaridar Leadership Sam Nda Isaah.
Ga yadda sakamakon yake a halin yanzu.
Muhammadu Buhari - 3430
Rabi'u Musa Kwankwaso - 974
Rochas Okorocha - 624
Atiku Abubakar - 954
Sam Nda Isaah - 10
Jam'iyyar PDP mai mulki a Najeriya ta kammala zaben fidda gwaninta, inda shugaba mai mulki Goodluck Jonathan ya karbi akalar takarar, tare da mataimakinshi Namadi Sambo.
Jaddawalin Sakamakon Zaben Fidda Gwani na Tsayawa Takarar Shugaban Kasa a APC, daga wakilin Muryar Amurka Hassan Umaru Tambuwal.