Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sakataren Harkokin Wajen Amurka ya ce kisan kare dangi aka yi a Myanmar


Rex Tillerson, sakataren harkokin wajen Amurka
Rex Tillerson, sakataren harkokin wajen Amurka

Rex Tillerson sakataren harkokin wajen Amurka ya ce abun da aka yiwa 'yan kabilar Royhingya a jihar Rokhine a kasar Myanmar babu shakka kisan kare danji ne

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Rex Tillerson ya ce tashin hankalin da ake yi a jahar Rakhine ta kasar Myanmar, inda ake auna al’ummar Musulmi, ya zama kisan kare dangi.

“Bayan cikakken nazarin bayanai sihihai, ta bayyana a fili cewa al’amarin nan na arewacin jahar Rakhine ba wani abu ba ne illa kisan kare dangi ake ma Musulmi ‘yan Rohingya,” a cewar Tillerson a wani rubutaccen bayanin daya gabatar jiya Laraba.

Jami’an Amurka sun yi ta binciken musabbabin hare-haren da su ka kai ga kashe daruruwan ‘yan Rohingya da kuma tilasta ma wasunsu fiye da 600,000 gudu zuwa sansanonin ‘yan gudun hijira da ke kasar Bangladesh.

Sanarwar ta jiya Laraba ce karon farko da Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ayyana wannan tashin hankalin a zaman kisan kare dangi. Jami’an da su ka yi ma manema labarai karin bayanidaga bisani, sun jaddada cewa daga yanzu haka za a rika bayyana al’amarin.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG