Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sakataren Harkokin Wajen Amurka John Kerry Zai Fara Ziyararsa Ta Farko Zuwa KetareTun.....


Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry.
Sabon sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry zai fara ziyarar aikinsa ta farko zuwa kasashen ketare, tun bayanda ya karbi aiki daga hanun Hillary Clinton ciikin watan nan.

Ana sa ran yau lahadi zai bar Washington zuwa Ingila a rangadin kasashe tara cikin kwanaki 11.

Ma’aikatar harkokin wajen Amurka tace rikicin Syria zai kasance babban kan ajendarsa a tattaunawar da zai yi da jami’an kasa da kasa da zai gana da su a lokacin wannan ziyara.Haka kuma Kerry yana da niyyar ganawa da shugabannin gamayyar ‘yan hamayya na Syria.

Daga London Kerry zai nufi Berlin, da Paris, inda zai tattauna kan hadin kai tsakanin Washington da Paris da wasu kasashe wajen baiwa Mali gotyon baa a rikici da kasar take fuskanta.

Daga nan Mr. Kerry zai kai ziyara Roma, da Turkiyya, da Masar, inda ma’aikatar harkokin wajen Amurka tace zai jaddada muhimmancin hada kai, sannan zai gana da jami’an kungiyar hada kan kasashen larabawa da nufin shawarwari kan hanyoyin tunkarar kalulable da duka sassa suke fuskanta a yankin.

Kerry zai kammala rangadinsa a Saudiyya da Abu Dhabi, sannan ya yada zangonsa ta karshe a Qatar.
XS
SM
MD
LG