Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Ya Gana Da Takwaran Sa Na Rasha Kan Tsagaita Wuta A Syria.


Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ya gana da ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov a Geneva yau Juma’a a wani kokarin shirin tsagaita wuta a Syria

Ma’aikatar harakokin wajen Amurka tace tattaunawar tasu zata mai da hankali ne akan yadda za’a rage tashin hankali, fadada daman kai kayan agaji ga mutanen Syria da kuma neman hanyar warwaren wannan yakin basasa da yaki karewa.

Kerry da Lavrov sun hadu a lokuta da dama makwanni biyu da suka wuce a Geneva da kuma a taron manyan kasashe na G20 a China, amma har yanzu an kasa cimma matsaya kan tsagaita wutar.

Jami’an diplomasiya na Amurka sun zanta da Murayar Amurka kuma sun bayyana rashin jin dadinsu da takwarorinsu na Rasha wanda suke zarginsu da mai da hannun agogo baya akan wasu muhimman baututuwa da aka dace a kansu a cikin wannan lokaci.

Rasha dai itace babban kawar gwamnatin Syria a cikin yakin, a papatawa da take yi da kungiyoyin yan tawaye da IS masu kokarin hambarar da gwamnatin shugaba Assad.

Ita dai Amurka tana goyon bayan yan adawa ne tare kuma da zargin Rasha da da kara dagula a’amura a Syria.

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG