Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Ya Kai Ziyara Fadar Sarkin Musulmi A Sokoto


 John Kerry, sakataren harkokin wajen Amurka da Mai Martaba Sarkin Musulmi Sa'ad Abubakar III a fadar sarkin dake Sokoto
John Kerry, sakataren harkokin wajen Amurka da Mai Martaba Sarkin Musulmi Sa'ad Abubakar III a fadar sarkin dake Sokoto

Cikin watanni ishirin da yake rike da mukamin sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry ya kai ziyara Najeriya sau ukku amma wannan ne karon farko da zai ziyarci Mai Martaba Sarkin Musulmi a fadarsa dake Sokoto

John Kerry ya bayyana wannan ziyara tasa zuwa Sokoto a zamar ta musamman.

Yayinda yake jawabi wa sarakuna da shugabannin al'ummomi daban daban a fadar mai alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa'ad Abubakar III, John Kerry ya tabo alamura da dama da suka hada da ilimi, da tattalin arziki da kuma sha'anin tsaro da yaki da ta'adanci, musamman kungiyar Boko Haram a arewa maso gabashin kasar.

John Kerry a Sokoto yana jawabi
John Kerry a Sokoto yana jawabi

Yace kungiyar Boko Haram bata da wata manufa illa ta kashe malamai, ta sace dalibai da yiwa mata fyade da kuma karkashe mutanen da basu ji ba ba su gani ba, wadanda mafi akasarinsu musulmai ne.

Akan haka John Kerry yace gwamnatin

Amurka ta kuduri anniyar cigaba da tallafawa Najeriya wajen kawo karshen zubda jini da sunan tsatsauran ra'ayin addini, musamman wajen samarda ingantacen tsarin yaki da ta'addanci.

John Kerry a Sokoto yana cigaba da jawabinsa
John Kerry a Sokoto yana cigaba da jawabinsa

Yace dalili ke nan da ya sa gwamnatin Amurka ta fito da wani sashe na yaki da ta'addanci da tsatsauran ra'ayin addini a farkon wannan shekara, kuma take aiki tukuru domin aiwatar da shirin.

John Kerry yayi anfani da damar da ziyarar ta bashi inda ya jinjinawa Mai Alfarma Sarkin Musulmi Sa'ad Abubakar III akan dagewa da yayi wajen hada kawunan 'yan Najeriya mabiya addinai daban daban tare da manufar tabbatar da zaman lafiya a Najeriya da sauran kasashen duniya.

A nashi bangaren Mai Alfarma Sarkin Musulmi Sa'ad Abubakar III ya yaba da kulawa da kuma tallafin da gwamnatin kasar Amurka take ba Najeriya. Amma kuma ya bukaci hukumomin Najeriya din da su kara zane damtse domin anfana da tallafin na kasar Amurka.

Yace takwarorinmu dake bamu tallafi irin kasar Amurka zasu iya kara samun karfin gwuiwar tallafawa ne kawai idan mu kuma mun basu damar yin haka.

Tun farko dai sai da Sakatare John Kerry, wanda Gwamnan Sokoto Aminu Waziri Tambuwal da takwaransa na jihar Zamfara Yari Abubakar suka raka, ya gudanar da wani taron siri da wasu shugabannin addinan musulunci da kirista a fadar Sarkin Musulmi.

Ga rahoton Murtala Faruk Sanyinna da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:52 0:00

XS
SM
MD
LG