Accessibility links

Sakataren Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka Ya Nemi Hadin Kan Kasar Japan

  • Grace Alheri Abdu

Sakateren Ma'aikar Harkokin Wajen Amurka John Kerry
Sakataren ma’aikatar harkokin wajen Amurka John Kerry ya gana da takwaransa na kasar Japan a birnin Tokyo Fumio Kishida da nufin hada kai wajen aikawa da sako mai karfi ga Pyongyang, yayinda Koriya Ta Arewa take barazanar gwada makami mai linzami.

Bayan tattaunawar, Kerry yace a shirye Amurka take ta kare Japan. Ya kuma kara da cewa, za a sake wani zaman tattaunawa da ya kunshi manyan jami’an gwamnati da nufin neman hanyar warware takardamar da ake yi a yankin Koriya cikin ruwan sanyi.

Kerry ya kuma bayyana cewa, jami’an diplomasiyan biyu sun sami ci gaba dangane da batun girke jami’an sojin amurka a Okinawa, da ya hada da sake matsugunin sansanin mayakan dake Futenma.

Dangane da tsibiran Senkaku kuma wanda Beijing da Tokyo suke ikirarin mallaka, Kerry yace Washington bata da wani ra’ayi kan diyaucin tsibiran, sai dai ta san cewa, Japan ke gudanar da lamura a wurin. Ya bayyana cewa, Amurka tana adawa da duk wani yunkurin da kasa daya zata yi na gaban kanta da nufin kwace tsibiran da ake takaddama a kai.

Kerry ya isa Tokyo ne yau Lahadi bayan tashinsa daga Beijing. Zai kuma gana da PM Shinzo Abe gobe Litinin domin tattaunawa kan ayyukan makaman nukiliya na Koriya Ta Arewa.

Japan wadda take inda makaman Koriya Ta Arewa masu linzami zasu iya isa, ta kewaye babban birnin kasar da nata na’urorin kange makaman.

A Beijing kuma, Kerry da takwaransa na kasar China, Yang Jeichi, sun amince zasu yi aiki tare wajen warware rikicin yankin Koriya. Jami’an diplomasiyan biyu sun bayyana jiya asabar cewa, suna goyon bayan raba yankin Koriya da makaman nukiliya.
XS
SM
MD
LG