Wani kwararre a fannin harkokin tsaro a Najeriya Janar Abdul’razak Umar ya bayyana cewa, sake shugaban hukumar tsaron ciki ta SSS ba wani abu ba abin mamaki bane.
Bisa ga cewarsa, shugaba Muhammadu Buhari yana bukatar mutum da ya yarda da shi, ya rike wannan mukamin. Yin garambawul a hukumar yana da
sauki, kasancewa, akwai ka’idoji da kowacce hukuma da aka kafa ya kamata tabi wajen gudanar da ayyukanta.
Bisa ga cewarsa, hukuma ko ma’aikata bata ingantuwa sai tabi ka’idojin da aka kafata. Saboda haka abinda ake bukatar yi shine abi ka’idojin da aka shinfida na gudanar da ayyukan hukumar, domin an tsara ayyukanta ne bisa la’akari da bukatun da kuma gurorin da ake neman cimma da kafa hukumar.
Janar Umar yace, hukumar SSS ce ya kamata tayi bincike a kasa kasa a yakin da ake yi da kungiyar Boko Haram har su ciwo lagon abin kafin a tunkare su, amma idan za a rika kama-saki, babu inda za a je.
Ga hirar su da wakilin Sashen Hausa Umar Faruk