Accessibility links

Sakon Barka Da Sallah Daga Darektan Muryar Amurka

  • Halima Djimrao

Darektan gidan rediyon Muryar Amurka David Ensor

David Ensor ya ce a madadin duka ma'aikatan Muryar Amurka ya na yin barka da sallah ga masu kallon mu da sauraren mu a kasashen Musulmi

Shugaban gidan rediyon Muryar Amurka David Ensor ya aike da sakon barka da sallah ga daukacin masu kallon mu da sauraren mu tare da sallama irin ta Islama. Ya ce a cikin watan azumin Ramadan ma'aikatan Muryar Amurka sun gabatar mu ku da labarai daga sassan duniya daban-daban, da kuma labarai da shirye-shirye game da yadda Musulmi ke bauta a cikin wannan wata mai daraja da alfarma. David Ensor ya ce a madadin duka ma'aikatan Muryar Amurka, ya na fata wadannan labarai da shirye-shirye su karfafa dankon zumunci tsakanin mu da ku masu saurare a wannan lokaci na taimakekkeniya da sabunta tuba da neman tsarkaka, daga karshe darektan Muryar Amurka, David Endsor ya kammala da cewa, mun gode mu ku da sauraren Muryar Amurka.
XS
SM
MD
LG