Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sam Ndah Isiah Ya Fito Takarar Shugaban Kasa.


Wasu Jaridun Najeriya.

Mr Sam Ndah Isiah yace idan har Allah Ya sa jam'iyyar APC ta bashi takarar shugabancin Najeriya to babu shakka zai taka rawar gani.

Gangamin na ayyana takarar shugabancin Najeriyar ya kuma janyo wasu 'yan takara a inuwar jam'iyyar zuwa taron, cikinsu harda tsohon mataimakin shugaban Najeriya Alhaji Atiku Abubakar, wanda yace dukkansu wadanda suke takarar shugabancin Najeriya a inuwar jam'iyyar APC duk wanda Allah Ya baiwa takarar babu wanda baifi shugaban kasa Goodluck Jonathan ba.

A nasa jawabin, Gwamnan jihar Rivers Rotimi Ameachi, ya yabawa bangaren shari'a, saboda hukuncin da ta yanke na tabbatar da abunda doka tace cewa babu wanda yake da ikon cewa a bude majalisa in banda kakakin majalisar wakilai ba. Da ya juya kan batun janye jami'an tsaro wadanda suke bada kariya ga kakakin majalisar wakilan Aminu Waziri Tambuwal, mataki da hukumomin tarayyar suka dauka bayan da Tambuwal ya canza sheka, Gwamna Rotimi yace matakin ya nuna cewa rundunar 'Yansandan Najeriya tana biyayya ne ga PDP ba 'yan Najeriya ba.

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG