Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sama da Matasa Maitan Sun Sami Jari A Jihar Borno.


Matasan da suka sami horo a jihar Borno

Gwamnatin jihar Borno tare da hadin guiwar hukumar raya kasashe ta Majalisar Dinkin Duniya UNDP, sun horas da wadansu matasa dari biyu da arba’in da tara kan sana’oin hannu dabam dabam .

An debi tsawon sama da wata shida ana horas da matasan da suka hada da maza da mata kan wadannan sana’oi da suka hada da dinki, da kanikanci da aikin kafinta, da walda da gyaran wayar hannu, da aikin gyaran kwano

Gwamnatin jihar Borno da hukumar rayar kasashen ta Majalisar Dinkin Duniya sun kuma mikawa matasan kayan aiki na miliyoyin nairori, daga bisani kuma gwamnan jihar Kashim Shetimma yace za a ba matasan ayyukan yi bisa ga sana’oin da suka koya.

A nata jawabin, wakiliyar Majalisar Dunkin Duniya, Mjihue Yukai ta kalubalancin matasan suyi amfani da horon da suka samu. Tace nasara ita ce sake yunkurowa duk lokacin da ka durkushe duk da yake ba abu ne mai sauki ba gudanar da rayuwarsu bisa sana’ar da suka koya.

Ko wanne mataki gwamnatin tabi na daukar matasan da aka koyawa sana’a?

Saurari cikakken rahoton Haruna Dauda Bi’u daga Maiduguri.

Matasa sun sami jari a jihar Borno-3:52
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG