Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sama Da Mutum 136 Sun Kamu Da Wata Cuta a China


Jami’an kiwon lafiya a birnin Wuham dake tsakiyar kasar China sun tabbatar da mutane 136 sun kamu da kwayar cutar da ake kira Corona virus, wata babbar annoba da ta barke a cikin kwanaki uku da suka wuce.

Hukumar kiwon lafiyar birnin Wuham ta ce jumullar mutane da suka kamu da cutar sun kai dari biyu, ciki har da wasu mutane biyu da suka kamu a Beijing da mutum daya a Shenzhen dake kudancin China.

Likitoci a birnin Wuham, birni mafi shahara na bakwai a China, sun kara kaimi wurin gwajin mutanen da ake zaton sun kamu da cutar sanyi. Likitocin suna kira ga jama’a suyi taka tsantsan da lafiyar su kana su rufe bakin su a duk lokaci da zasu yi atishawa.

A ranar Juma’a ne cibiyar kula da kare cututtuka ta Amurka, ta fara tantance lafiyar fasinjoji daga birnin Wuham na China zuwa filayen jiragen sama uku na nan Amurka da suka hada da San Francisco da Los Angeles da kuma New York. Haka zalika ake gudanar da irin wannan gwajin lafiyar fasinjojin Wuham a filayen saukar jirage saman Japan da Thailand da South Korea da kuma Singapore.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG