Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Samamen Hadin Guiwar Mali da Mauritania Ya Halaka 'Yan Al-Qaida 15


Wani sansanin horon mayaka irin wadanda al-Qaida ke da su har a arewacin Afirka
Wani sansanin horon mayaka irin wadanda al-Qaida ke da su har a arewacin Afirka

Mayakan Al-Qaida 15 sun sheka lahira bayan karawar su da sojojin Mali da na Mauritania.

Gwamnatin kasar Mauritania ta ce an kashe mayakan al-Qaida 15, an kama wasu 9 a cikin wani samamen hadin guiwa da Mali wanda aka kai har wani sansanin ta'addancin al-Qaidar da ke Mali.

Wani Kanal din soji ya fada a jiya Lahadi cewa an kashe sojojin Mauritania biyu ma a cikin harin na ranar Jumma'a da aka kai sansanin yankin gandun dajin Wagadou dake daf da kan iyakar Mali da Mauritania.

Ya ce haka kuma sojojin Mali sun kama mayakan al-Qaida 9.

Sojojin kasashen biyu, wato Mauritania da Mali, su ne su ka kaddamar da samame da nufin yin turnukun kakkabe 'yan al-Qaidar kasashen Musulmin arewacin Afirka daga sansanonin su da ke daf da yankunan kan iyakokin kasashen.

'Yan ta'addan reshen kungiyar al-Qaidar arewacin Afirka na yin amfani da sansanonin su na kai hare-hare a yankin.

XS
SM
MD
LG