Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Jacob Zuma Yana Kashedi Ga NATO kar....


Shugaban Afirka ta kudu Jacob Zuma yake hanu da shugaba Gadhafi,kamin taro d a suka yi cikin watan jiya a Tripoli.

Shugaban Afirka ta kudu Jacob Zuma ya gargadi NATO kada tayi amfani da karfin sojinta ta kashe shugaban Libya Moammar Gadhafi.

Shugaban Afirka ta Kudu Jacob Zuma, ya gargadi kungiyar tsaro ta NATO, da kada tayi amfani da karfinta na soji ta kashe shugaban Libya Moammar Gadhafi.

Yau lahadi ne shugaban Afirka ta kudun, yayi magana a Pretoria, yayinda wani kwamitin kungiyar tarayyar mai fada a ji, yake shawarwari kan hanyoyin warware rikicin kasar Libya, wadda ya dauki wata hudu ana gwabzawa, a can gabashin Afirka.

Mr. Zuma yace kudurin majalisar dinkin duniya da ya bada izinin daukar matakin soja a Libya, an zartas da shi ne da nufin kare rayukan al'umar kasar, ba an amince da shi da nufin "canza gwamnati, ko kashe shugabannin siyasar kasar ba".

Kungiyar NATO ta karyata cewa tana auna hari kan Gadhafi bayan wani hari da ta kai ranar daya ga watan Mayu, da gwamnatin Libyan tace ya kashe wasu iyalan shugaba Gadhafi hudu. A lokacin Rasha ta bayyana shakkunta kan musanta zargin da NATO tayi.

Mr. Zuma yace kungiyar AU ta hakikance cewa duk wata hanyar warware wan nan rikici tilas ta kasance ta siyasa, kuma hakan "yana hanun 'yan kasar Libya."

Yace Tarayyar Afirka tana son ganin an tsagaiata wuta,san nan a aiwatar da sauye sauyen siyasa, daga bisani 'yan kasar cikin walwala, su zabi shugabbinsu.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG