Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Samar Da Ababen More Rayuwa Zai Ba ‘Yan Najeriya Damar Da Za Su Kula Da Kansu – Buhari


Shugaba Buhari a taron Paris (Facebook/Gwamnatin Najeriya)

Shugaban Najeriya ya yi wadannan kalaman ne yayin da matsalar rashin tsaro a kasar ke ci gaba da ta'azzara, ko da yake hukumomin kasar sun ce suna shawo kan lamarin.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce cikin shekara shida da suke mulki, gwamnatinsa ta dukufa ne wajen ganin ta samar da ababen more rayuwa ga ‘yan kasar.

Cikin wata sanarwa da kakakinsa Femi Adesina ya fitar a ranar Alhamis, Buhari ya ce idan babu ababen more rayuwa a kasa, babu yadda za a samar da ci gaba mai dorewa.

“Lura da dumbin yawan da muke da shi a wannan kasa ta mu, muna bukatar hanyoyi, hanyar dogo, wutar lantarki, filayen tashin jirage da gidaje. Wadannan sune ayyukan da muka dukufa wajen ganin mun samar cikin shekara shida da muka yi.”

“Idan aka samar da wadannan ababen more rayuwa, mutanenmu za su iya kula da kansu.” Buhari ya ce.

Shugaba Buhari a cewar sanarwar ta Adesina, ya bayyana hakan ne yayin da ya gana da shugaban bankin Islama na IDB Dr. Mohammed Al – Jasser a gefen taron samar da zaman lafiya a duniya da ke gudana a birnin Paris na kasar Faransa.

“Muna matukar fadin-tashin ganin mun samar da wadannan ababen more rayuwa, saboda idan babu su, babu yadda za a samu ci gaba mai dorewa.” In ji Buhari.

Shugaban na Najeriya ya kara da cewa, “kuma jama’ar kasarmu na ganin sabbin ci gaban da ake samu daidai da arzikin da muke da shi, kuma mun taka rawar gani daidai gwargwado.”

A nasa bangaren, shugaban bankin na IDB, Dr. Al-Jasser ya jinjinawa gwamnatin Buhari da irin kokarin da take yi wajen aiwatar da tsare-tsarenta da samar da ababen more rayuwa.

“Najeriya muhimmiyar kasa ce a gare mu, ta kuma kamaci a ba ta duk irin taimakon da take bukata.” In ji Al-Jasser.

Ya kara da cewa dalilin kafa bankin shi ne a taimakawa abokanan hulda yana mai cewa bankin zai ci gaba da tallafawa Najeriya.

Shugaban Najeriya ya yi wadannan kalaman ne yayin da matsalar rashin tsaro a kasar ke ci gaba da ta'azzara, ko da yake hukumomin kasar sun ce suna shawo kan lamarin.

Dubi ra’ayoyi

Ramaphosa Ya Kai Ziyara Najeriya

Lokacinda Ramaphosa Ya Isa Abuja
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:37 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Ana ci gaba da muhawara a kan ko daga wane yanki na Najeriya yakamata shugaban kasar na gaba ya fito

Karin bayani akan Bidiyo

Zabarmawa, Zabuwa, Ghana

Yadda Aka Gudanar Da Wasan Zabuwa A Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:14 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Sabbin kotunan soji a Maiduguri za su yi shari’a ga kanana da manyan sojoji

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG