Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Samar Da Ilimi Ga Kananan Yara a Borno


Schoolgirls play outside El-Kanemi Islamic School, where both Western and Islamic curriculums are taught, in Maiduguri.
Schoolgirls play outside El-Kanemi Islamic School, where both Western and Islamic curriculums are taught, in Maiduguri.

Tun bayan da Najeriya ta tsinci kanta a cikin rikicin Boko Haram a shekarar 2009, ya zuwa yanzu dubban mutane ne suka rasa rayukansu baya ga wasu miliyoyi da suka fice daga muhallansu domin kaucewa tashe tashen hankula.

Mafi aksarin wannan matsala ta rashin tsaro ta fi addabar yankin arewa maso gabashin kasar ne musamman a jihohin Borno da Yobe, sai kuma jihar Adamawa.

Baya ga asarar rayuka da aka yi a wannan lamari mai cike da sarkakiya, rikicin ya yi tasiri kwarai akan harkokin kasuwancin yankunan da kuma harkar ilimi.

Yanzu haka dubun dubanta yara kanana da dama ne ba sa zuwa makaranta saboda rashin tsaro a yankunansu, lamari da ya sa suke ta galantoyi akan tituna yayin da suke zaune a sansanonin ‘yan gdun hijra da hkumomi suka samar.

Ganin cewa harkar ilimi batu ne mai mahimmanci musamman ga yara kanana, wata kungiya mai zaman kanta da ake kira Creative Associates International da ke birnin Washington a Amurka, wacce kuma ke samun tallafi daga hukumar tabbatar da raya kasashe ta USAID, ta kirkiro wasu wurare da ake koyar da yara ilimin zamani.

Baya ga haka akwai kungiyoyi irin su Red Cross da ke tallafawa, ibda suma sukan sun baiwa wasu mata da suka rasa mazanjensu a wannan rikicin jari domin su fara kasuwancin da zai rike su.

Domin jin yadda makarantar ke gudana da kuma yadda matan da ake tallafawa suke neman taro da sisi, saurari wannan fassarar rahoto da wakilin Muryar Amurka Michael Lipin ya hada mana:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:33 0:00
Shiga Kai Tsaye

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG