Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

SANARWA:  Abu Ubayda Yusuf Al-Anabi


Sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken
Sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken

A shekarar 2015, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ayyana al-Anabi a matsayin Rikakken Dan Ta’addan Duniya, inda ta rufe duk dukiyarsa da bukatunsa a cikin dukiyar da ke karkashin ikon Amurka

Abu Ubaydah Yusuf al-Anabi shi ne shugaban kungiyar ‘yan ta'adda ta al-Qaida a yankin Maghreb, wanda aka fi sani da AQIM. Daga cikin ayyukan ta'addancin da take yi, AQIM kan sace tare da kashe Amurkawa.

Shirin Bada Tukuici Don Adalci na Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka zai ba da ladan dala miliyan 7 ga duk wanda ya ba da labarin da zai kai a ga gano inda Abu Ubaydah Yusuf al-Anabi yake.

An sanar da Al-Anabi a matsayin shugaban AQIM a watan Nuwamba na 2020, bayan da aka kashe jagorar kungiyar na farko, Abdelmalek Droukdel a watan Yunin 2020. Al-Anabi ya rantse ga biyayya ga shugaban al-Qaida Ayman al-Zawahiri a madadin AQIM kuma ana sa ran zai taka rawa a cikin tsarin al-Qaida a duniya kamar yadda Droukdel ya yi.

Al-Anabi ɗan ƙasar Aljeriya ne, an haife shi a shekarar 1969. A baya ya rike mukamin shugaban Majalisar AQIM ta sanannun mutane kuma ya yi aiki a Majalisar Shura ta AQIM. Bugu da kari, ya kasance shugaban yada labarai na AQIM. An kuma san shi da sunan Abou Obeida Youssef al-Annabi ko Yezid Mebrak.

A shekarar 2015, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ayyana al-Anabi a matsayin Rikakken Dan Ta’addan Duniya, inda ta rufe duk dukiyarsa da bukatunsa a cikin dukiyar da ke karkashin ikon Amurka kuma ta hana mutanen Amurka yin hulda da shi. A 2016, an sanya shi a cikin jerin takunkumi na Majalisar Dinkin Duniya, abin da ya yi sandiyyar dakatar da dukiyarsa na kasa da kasa, hana tafiye-tafiye, da kuma takunkumin sayen makamai.

Tun lokacin da aka fara a shekarar 1984, Shirin Bada Tukwici Don Adalci, wanda Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ta Tsaro ta diflomasiyya ke gudanarwa, ya biya sama da dala miliyan 200 ga sama da mutum 200 da suka bayar da bayanan da suka taimaka wajen gurfanar da 'yan ta'adda a gaban shari'a ko hana aikata ta'addanci a duniya.

Bi shirin akan Twitter a: https://twitter.com/rfj.usa.

Muna ƙarfafa duk wanda yake da bayani game da ɗan ta'adda Abu Ubaydah Yusuf al-Anabi, da ya rubuta sakon tes zuwa ga tukwici don Adalci ta hanyar sakon Telegram, ko WhatsApp a + 1-202-702-7843.

Duk bayanan da mutum ya bayar za su kasance sirri.

XS
SM
MD
LG