Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sanata Abdullahi Adamu Ya Zama Sabon Shugaban APC A Najeriya


Sabon shugaban jam'iyyar APC, Sanata Abdullahi Adamu
Sabon shugaban jam'iyyar APC, Sanata Abdullahi Adamu

Ayyana Sanata Adamu a matsayin shugaban jam’iyyar na zuwa ne kusan shekaru biyu bayan da aka rusa kwamitin gudanarwar Adams Oshiomole.

Tsohon gwamnan jihar Nasarawa, Sanata Abdullahi Adamu, ya zama sabon shugaban jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya.

Shugaban kwamitin zaben jam’iyyar, Gwamnan jihar Jigawa, Abubakar Badaru ne ya sanar da zabin Sanata Adamu a matsayin shugaban jam’iyyar.

Dama jam’iyyar ta APC ta sadaukar da mukamin shugaban jam’iyya ga yankin tsakiyar arewacin Najeriya.

Kuma tun gabanin babban taron rahotanni da dama ke cewa Sanata Adamu wanda za a ba mukamin.

Tsohon gwamnan na Nasarawa ya zama shugaban na APC ne a babban taron da jam’iyyar ta gudanar a ranar Asabar a Abuja, inda aka ayyana shi a matsayin shugaban jam’iyyar ba tare da wata hamayya ba

Ayyana Sanata Adamu a matsayin shugaban jam’iyyar na zuwa ne kusan shekaru biyu bayan da aka rusa kwamitin gudanarwar Adams Oshiomole.

Ko da yake, Sanata Adamu zai karbi shugabancin jam’iyyar ne daga hannun gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni, wanda ya jagoranci jam’iyyar a matakin rikon kwarya bayan da aka rusa kwamitin gudanarwar Oshiomole a 2020.

Rahotanni sun yi nuni da cewa tun gabanin a je ga bayyana wanda zai zama shugaban jam’iyyar, dukkan ‘yan takarar da suka nemi mukamin tare da Sanata Adamu suka janye takararsu.

An dai yi ta kai ruwa rana gabanin wannan babban taro na APC, inda wasu suka yi ta nuna adawa da tsarin bai wa mutum kujerar ba tare da ya fafata da sauran ‘yan takara ba.

XS
SM
MD
LG