Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sanata John McCain Na Fama Da Sankarar Kwakwalwa


Kumburin da likitoci suka gano a cikin kwakwalwar Sanata Johan McCain na jam'iyyar Republican na tattare da illa.

An gano cewa sanannen dan majalisar dattawan Amurka, Sanata John McCain yana fama da sankarar kwakwalwa, a cewar wani asibiti na Mayo dake birnin Phoenix yau Laraba.

An gano wani mummunan kumburi mai illa a cikin kwakwalwar tashi bayan da aka yiwa Sanatan mai shekaru 80 na jam’iyyar Republican daga jihar Arizona wani aiki a makon da ya gabata don a cire masa wani gudajin jini da ya taru a gefen idonsa na hagu.

Wata sanarwa daga ofishin sanatan ta ce “likitocin Sanata McCain sun tabbatar da cewa yana samun sauki sosai kuma yanayin lafiyarsa yanzu yana inganta sosai.”

McCain dai, gwarzon yakin Vietnam ne wanda ya kasance dan majalissa a Amurka fiye da shekaru 30, kuma an ce ta yiwu iyalinsa su duba yiwuwar yin amfani da wasu magungunan, wanda yawancin lokuta zasu hada da amfani da karfin hasken laser wajen nema mashi lafiya.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG