Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Mutanen Kauyuka Na Hada Baki da Barayi - Dan Ali


Ministan Tsaron Najeriya Janar Mansu Dan Ali

Cikin firar da yayi da Muryar Amurka a taron Majalisar Dinkin Duniya ministan tsaron Najeriya Janar Mansur Dan Ali yace wasu mutane dake zaune a kauyuka suna hada baki da barayi a arewacin kasar suna satar shanu ko mutane.

Ministan yayi misali da wurin da ya fito, Birnin Magaji, inda yace mazauna wasu kauyukan suna hada baki wurin kunkuma sata musamman satar shanu, hatta a kauyensa an samu irin wadannan mutanen.

Yace sai da gwamnatin Buhari ta zo aka yi hobasan shawo kan lamarin. Yace sun yi atisahi a duk dazuzukan kamar a jihar Zamfara da zummar fatattakan barayin.

Yace idan sojojinsu zasu je wurin sai su yi masu waya suna zuwa. Kwanakwanan nan suka je kauyen Dumburum dake cikin karamar hukumar Zurmi inda suka samu shanun da aka sace wajen dubu ukku amma mutanen sun gudu.

Yanzu gwamnati na shirin kara sojoji a jihar Zamfara domin bataliya guda bai isa ba.

Dangane da yaki da Boko Haram yace suna iyakar kokarinsu. Duk abun da Boko Haram ke cewa yanzu farfaganda ce kawai. A kan sojoji kuma yace duk abun da suke bukata ana basu daidai gwargwado.

Ga rahoton Ladan Ibrahim Ayawa da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:07:00 0:00

please wait

No media source currently available

0:00 0:07:00 0:00

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG