Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sarki Sunusi II Ya Karbi Sandar Mulki


“Ni Muhammadu Sunusi na biyu, na rantse da Allah, zanyi aiki sosai da gaskiya, ga gwamnatin Jihar Kano, a mukamina na Sarkin Kano. Kuma zan kiyaye, tsarin mulki kamar yadda doka ta kafa.”

Mai Martaba Sarkin Kano kennan, Mallam Muhammadu Sunusi na biyu, yake karbar rantsuwar kama aiki a gaban babban limamin Kano, Farfesa Muhammad Zaharaddeen a lokacin bukin bashi sandar girma a babban dakin taro dake gidan gwamnatin Jihar Kano.

Bayan kammala rantsuwar, madakin Kano, daya daga cikin masu zaben Sarki a majalisar masarautar Kano, Mallam Yusuf Labahani ya mika wukar dabo, da rawani da kwari da baka, da al-kyabba, da sauran kayayyakin da sarauta da al-ada ta tanada.

A watan Yunin shekarar bara ne Mallam Muhammadu Sunusi na biyu ya zama Sarkin Kano na hamsin da bakwai biyo bayan rasuwar Sarkin Kano, marigayi Alhaji Ado Bayero.

Gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso shine ya mika sandar ga sabon Sarkin na Kano.

“Mai martaba Alhaji Ado Bayero, yayi aiki babu dare babu rana a jihar nan, da kasar nan, domin taimakawa al-umma. Muna yiwa mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi na biyu fatan alheri a addu’a.

Baki daga ciki da wajen Najeriya ne suka hallarci taron wadanda suka hada da Jakadan Amurka a Najeriya, Mr. James Entwistle da tsofaffin shuwagabannin Najeriya, kamar Janar Muhammadu Buhari, Yakubu Gowon da Sarkin Musulmi Muhammadu Sa’ad Abubakar, da sauran sarakuna daga arewaci da kudancin Najeriya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:27 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG