Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sarkin Biu, Alhaji Mai Umar Mustapha Aliyu Ya Rasu


Sarkin Biu, Alhaji Mai Umar Mustapha Aliyu

Kamar yadda aka saba a duk lokacin da aka yi rashin iyayen kasa, dinbin mutane sun yi cincirindo wajen jana'izar Mai Martaba Sarkin Biu, Mai Umar Mustapha Aliyu, duk kuwa da wannan marra da ake ciki, saboda nuna girmamawa da kuma alhini.

Allah ya yi wa Sarkin Biu, mai martaba Mai Umar Mustapha Aliyu rasuwa.

Alhaji Mai Umar Mustapha Aliyu, basaraken gargajiya na garin Biu a jihar Borno, ya mutu yana da shekara 80.

Ya rasu ne da daren jiya Litinin bayan wata gajeriyar rashin lafiya.

Alhaji Mai Umar Mustapha Aliyu ya hau karagar mulki a shekarar 1989.

Masarautar Biu, masarauta ce ta gargajiya dake garin Biu a jihar Borno, Najeriya.

Sarkin Biu, Alhaji Mai Umar Mustapha Aliyu
Sarkin Biu, Alhaji Mai Umar Mustapha Aliyu

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG