Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sarkin Katagum Muhammad Kabir Ya Rasu


Gwamnan jihar Bauchi M.A. Abubakar, na daya daga cikin mutanen da ake sa ran za su halarci jana'izar marigayi Sarki Kabir na Katagum

Bayan fama da ya yi da doguwar jinya, Allah ya yi wa Mai Martaba Sarkin Katagum Muhammad Kabir Umar rasuwa. Sarki Kabir ya rasu ne a gida bayan ya kwashe shekaru 37 yana mulkar masarautar.

Rahotanni daga jihar Bauchin Najeriya da ke arewa maso gabashin kasar na cewa, Allah yi yiwa mai Martaba Sarkin Katagum Alhaji Muhammad Kabir Umar rasuwa.

Sarki Kabir ya rasu ne bayan ya yi fama da wata doguwar rashin lafiya a gida.

Ya kuma kwashe shekaru 37 akan karagamar mulki.

Ana sa ran gobe Lahadi, za a yi jana’izarsa da safe.

Wakilinmu Abdulwahab Muhammad ya tattauna Galidaman masarautar ta Katagum, Usman Mahmud Abdullahi, wanda ya tabbatar da rasuwar marigayin.

“An zauna da shi lafiya, mutum ne mai son ‘yan uwansa da talakawansa, saboda haka muna cikin takaicin rashinsa.” Inji Galadima Abdullahi.

Saurari cikakkiyar hirar Abduwahab da Galadima Abdullahi:

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:30 0:00

Facebook Forum

Bidiyo

Yadda Wani Mutum Ya Mari Shugaban Faransa Emmanuel Macron
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:37 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Marigayi TB Joshua
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:27 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Gidajen Rediyon Najeriya Sun Gana Da Jami'an Diplomasiyya Kan Rikicin Twitter
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:51 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG