Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sarkin Musulmi Ya Ja Kunnen Matasa Kan Zaben 2019


Sarkin Musulmi Muhammadu Sa'ad Abubakar

Mai alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubabar, ya gargadi matasa gabannin zaben 2019, yayin da mai martaba Sarkin Kano Sunusi Lamido, ya yabawa shugabannin siyasa wajen martaba masarautun gargajiya.

Sarakunan dai sun hadu ne a wajen taron taya sarkin Ningi na 16, Alhaji Yunusa Danyaya, murnar cika shekaru 40 kan karagar masarautar Ningi.

Mai alfarma sarkin Musulmi ya bai wa al’umma shawarar cewa ganin yadda lokacin zabe ya karato, kada wanda ya bari shugabannin siyasa su yi amfani da kudi wajen jefa su wata harka da ba ta kwarai ba.

Haka kuma mai alfarman ya yi kira ga kowa ya je ya yi rijistar zabe domin yin amfani da ita wajen zaben shugabannin da suka dace.

A nashi jawabin mai martaba sarkin Kano, ya yabawa shugabannin siyasa da suke martaba masarautun gargajiya, don mutunta tarihi da kuma hadin kai don taimakawa al’umma.

Yayin wata hira da ya yi da Muryar Amurka, uban taro mai martaba Alhaji Muhammadu Yunusa Dan Yaya, ya yi tsokaci ne kan matsayar masarautun gargaji a tsarin mulkin kasa.

Domin karin bayani saurari cikakken rahotan Abdulwahab Muhammad.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:22 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG