Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Karin Makamai Zai Kara Zaburar Da Sojoji - Inji Buratai


Sojojin Najeriya

Hedikwatar rundunar sojojin Najeriya ta gudanar da wani taro kan samarwa dakarunta makamai don ci gaba da tunkarar matsalolin tsaro a kasar.

A wajen taron bita na kwana biyu babban Hafsan Sojojin kasa Na Najeriya, Janar Tukur Buratai, ya ce samarwa da sojoji makamai zai ‘kara kaimin rundunar wajen ci gaba da tunkarar kalubalen tsaro dake ‘kara kunno kai da canza salo a Najeriya.

Taron na sojojin na zuwa ne kwana guda bayan da gwamnatin Najeriya ta ce ta kebe dalar Amurka Biliyan daya don sayawa sojojin makamai.

A cewar shugaban kwamitin sojojin na Majalisar wakilan Najeriya, Rimande Shawulu, ta’addanci abu ne dake daukan dogon lokaci kafin a gama da shi.

A baya dai an taba ware makudan kudade domin sayawa sojojin Najeriya makamai amma kuma aka wawure kudin. Tsohon gwamnan mulkin soja na jihar Kano, kanal Aminu Isah Kwantagora, ya ce bashi da fargabar za a iya sake maimaita abin da ya faru a baya na wawure kudaden makaman.

Domin karin bayani saurari rahotan Hassan Maina Kaina.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:12 0:00

Facebook Forum

Bidiyo

Ko Kun San Irin Makaman Da Sojoji Ke Amfani Da Su Wajen Yaki Da 'Yan Bindiga A Jihar Zamfara?
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:31 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG