Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

"Tsabar Azaba Ta Sa Ni Amsa Laifin Da Ban Aikata Ba" - Matashi


Zaratan 'Yan Sandan Najeriya Na Musamman
Zaratan 'Yan Sandan Najeriya Na Musamman

A ci gaba da gabatar da korafe korafe da 'yan Najeriya ke yigaban kwamitin binciken zargin cin zarafi da ake ma rusassshiyar rundunar 'yan sandan musamman ta SARS a fadin Najeriya, a jahar Filato, kwamitin ya fara jin wasu zarge zarge masu tayar da hankali

Kwamitin sauraren korafe-korafen cin zarafi da ake zargin rusasshiyar rundunar ‘yan sanda ta musamman da ke yaki da miyagun laifuka wato SARS, da ke zama a jahar Filato na ci gaba da sauraren shaidu kan korafe-korafen da ke gabanshi.

Wasu da suka gabatar da korafin cin zarafi a gaban kwamitin sun bayyana irin ukubar da suka ce sun sha a hannun ‘yan sandan na SARS. Kama daga mai zargin ‘yan SARS sun nakasa shi da harbi da kuma bugu bisa zargi mara tushe zuwa mai cewa kaninsa ya mutu sanadiyyar harbin da ‘yan sandan SARS su ka yi masa a kai – da dai sauran zarge zarge masu karkada hanji.

Zanga zangar EndSARS a Jos
Zanga zangar EndSARS a Jos

Shugabar kwamitin, Mai Shari’a Philomena Lot, ta ce sun karbi takardun korafe korafe fiye da sittin daga jama’a, wadanda ke zargin cewa ‘yan sanda, musamman ma na rundunar SARS, da aka rusa daga baya, sun gallaza masu tare da tauye masu hakki babu gaira babu dalili.

Barista Yirvams Chamsan Jips, wanda ke halartar zaman kwamitin, ya ce yana da yakinin cewa wadanda suka gabatar da koke koken za su sami adalci.

Ga Zainab Babaji da cikakken rahoton ta sauti:

XS
SM
MD
LG