Jiya Lahadi Kuwait, wacce take shiga tsakani domin kawo karshen rikicin cikin lumana, ta nemi a kara wa'adin, jim kadan kamin karshen wa'adin farko.
Sanarwar da kamfanonin dillancin labaran Kuwait da Saudiyya suka bayar a sanyin safiyar yau Litinin din nan duk sun tabbatar da cewa an kara wa'adin har zuwa karshen yau Litinin.
Kasashen Saudiyya, da hadaddiyar daular kasashen Larabawa, da Bahrain, da Masar sun yanke huldar difilomasiyya da kasuwanci da Qatar ranar 5 ga watan Yuni, suna zargin gwamnatin Qatar da goyon bayan ta'addanci.
Qatar ta musanta zargin da wadan nan kasashe suka yi mata, tace zargin bashi da wani tushe. Ministan harkokin wajen wannan karamar kasa dake yankin na Gulf, Sheikh Mohammed bin Abdulrahman al-Thani, yace sharuddan da Saudiyya da kawayenta suke gindaya mata, da suka hada da janye sojojin Turkiyya daga kasar, da rufe tashar talabijin ta al-Jazeera da tauye dangantakar ta da Iran, suna da wuya ta mutunta su ba tareda ta sadaukar da diyaucinta ba.
Kasar Saudiyya da kawayenta da suke rikici ta fuskar difilomasiyya da Qatar, yau Litinin, suka kara wa'din da suka baiwa Qatar da sa'o'i 48 ta cika sharudda da suka gindaya mata.
WASHINGTON DC —
Maris 25, 2023
An Sami Karuwar Farashin Kayayyaki A Jamhuriyar Nijar
Maris 25, 2023
Shiye-Shiryen Shiga Watan Azumi A Kasar Ghana
Maris 25, 2023
Al'umomi Sun Koka Game Da Tashin Farashin Kayayyaki
Za ku iya son wannan ma
-
Maris 21, 2023
Saudiyya Ta Ce Ranar Alhamis Watan Azumi Zai Kama
-
Maris 17, 2023
Kotun ICC Ta Ba Da Izinin Kama Putin
-
Maris 13, 2023
Shugaba Buhari Ya Taya Xi Jinping Murnar Sake Lashe Zabe
Facebook Forum