Wannan wata gagarumar ci gaba ce ga matan kasar Saudiya da suke dogara ga danginsu dirobobi maza, ko shiga tasi ko kuma amfani da wadansu hanyoyi sufuri duk inda zasu je.
Farkon wannan watan gwamnatin Saudiya ta fara bada lasisin tuki ga mata wadanda aka basu lasisi a wadansu kasashe da suka hada da Birtaniya da Lebanon da kuma Canada. An yiwa matan gwajin tuki kadan kafin basu lasisin.
Sai dai galibin matan kasar basu riga sun sami lasisin tuki ba. Mata da dama basu sami damar samun horarwas tukin mot aba da aka gudanar na watanni kalilan.
Kamfanin dillancin labarai na Bloomberg yace hirar da ya yi da mata a Saudiya ya nuna galibi suna tababa a kan wannan ci gaban, dukansu suna dokin yin tuki saidai suna kuma so su kiyaye al’adunsu. Matan suka ce zai dauki lokaci kafin al’umma ta rungumi canjin.
Kamfanonin motoci suma suna kara damara kasancewa ana kyautata zaton cinikin motoci zai karu.
Farkon wannan shekarar kamfanin motoci na Ford ya dauki nauyin ba mata damar dandana tukin mota a birnin Jidda
Facebook Forum