Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Saudiyya Ta Zartar Da Hukuncin Kisa Kan Iraniyawa 6 Saboda Fataucin Kwayoyi


Noose rope
Noose rope

An zartarwa Iraniyawan hukuncin kisan ne a yankin Dammam dake gabar tekun Fasha na masarautar, saboda samunsu da laifin fataucin ganyen tabar wiwi cikin Saudiyya.

Kasar Saudiyya ta zartar da hukuncin kisa a kan wasu Iraniyawa 6 saboda fataucin kwayoyi, kamar yadda kamfanin dillancin labaran kasar (SPA) ta sanar a yau Laraba.

An zartarwa Iraniyawan hukuncin kisan ne a yankin Dammam dake gabar tekun Fasha na masarautar, saboda samunsu da laifin fataucin ganyen tabar wiwi cikin Saudiyya, kamar yadda ma'aikatar cikin gidan kasar ta bayyana a sanarwar da SPA ya wallafa ba tare da fayyace hakikanin ranar da aka zartar da hukuncin ba.

Mahukuntan birnin Riyadh sun zartar da hukuncin kisa a kan mutane 117 a 2024 saboda fataucin kwayoyi, a cewar alkaluman hukumar da kamfanin dillancin labaran AFP ya wallafa

A 2023, hukumomin Saudiyya sun kaddamar da gangamin yaki da kwayoyi da aka yi matukar yayatawa da ya sabbaba dimbin samame da kame.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG