Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Saura Kiris Clinton Ta Zama Mace Ta Farko A Takarar Shugabancin Amurka


Hillary Clinton ta jam'iyyar Democrats
Hillary Clinton ta jam'iyyar Democrats

Tsohuwar sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton ta kusa hada kan wakilai da ake bukata domin zama wacce zata yi takarar shugabancin Amurka karkashin jam'iyyar Democrat.

Amma tana fuskantar kalubale mai tsanani a jihar California, daga mutum daya da ya rage yana karawa da ita, watau Senata Bernie Sanders na jihar Vermont.

Madam Clinton wacce take kokarin zama mace ta farko da zata shugabanci Amurka kamin babban taron jam'iyyar a watan Yuli, yanzu tana da wakilai dubu biyu da dari uku da goma, cikin wakilai dubu biyu d a dari uku da tamanin da uku da ake bukata domin ta zama mace ta farko da wata babbar jam'iyyar siyasa a Amurka zata tsayar takarar shugabancin kasa. Babban abokin hamayyarta Bernie Sanders yana da wakilai 1,542.

A wani lamari kuma,alkalin wata babbar kotun Amurka ya bayyana kasidu fiyeda 400 dangane da yadda ma'aikatan tsohuwar jami'ar Trump suke amfani da matakai masu gauni na sa mutane su shiga jami'ar domin koyon dabarun sayen gidaje da wasu kadarori.

Sakin bayanan, wani bangare ne na shari'ar da wasu suka shigar suna zargin an yi musu zamba.

A wani taro da manema labarai a ofishinsa dake New York jiya Talata ya ci gaba da zargin alkalin da ya yanke shari'ar da cewa alkalin bashi da adalci.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG