Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Saura kiris shugaban Ivory Coast ya sauka daga kan mulki


Fararen kaya suna kaura da tarkacensu a birnin Abidjan, Ivory Coast.
Fararen kaya suna kaura da tarkacensu a birnin Abidjan, Ivory Coast.

Ministan harkokin wajen Faransa Alain Juppe ya fadawa Majalisar wakilan Faransa a yau talata cewa sau kiris Mr Gbagbo ya sauka daga kan mulki.

Ministan harkokin wajen Faransa Alain Juppe yace shugaban Ivory Coast Laurent Gbagbo yana dab da barin mulki. A yau talata Mr Juppe ya fadawa Majalisar wakilan Fanransa a birnin Paris cewa, saura kan shawarwarin da ake yi su shawo kan shugaba Gbagbo daya fice daga kasar, Wasu jami'an Faransa dana Ivory Coast sun fada cewa ana ci gaba da tattaunawa akan ficewar Mr. Gbagbo daga kasar. A yau Talata hafsan mayakan Gbagbo ya bukaci a tsagaita bude wuta a yayinda dakarun dake biyaya ga Ouattara suka kaiwa tungayen Gbagbo na karshe hare hare. Shugaba Gbagbo yaki ya ajiye ragamar mulki bayan da aka ayyana cewa Alassane Ouattara ne ya lashe zaben shugaban kasar da aka yi a watan nuwamba. A jiya litinin jiragen saman yakin Majalisar Dinkin Duniya masu saukar angulu suka kai hare hare fadar shugaba da gidan shugaba da kuma sansanonin sojojin shugaban. Baban sakataren Majalisar Dinkin duniya Banki Moon yace an kai hare hare ne da nufin hana sojojin Gbagbo amfani da manyan makamai wajen kaiwa farar hula da sojojin kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya hare hare.

XS
SM
MD
LG