Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sauyin Yanayi: Jihohi Sun Yi Taro


Taro Kan Dumamar Yanayi
Taro Kan Dumamar Yanayi

A ci gaba da daukar mataki da dan adam ke yi kan sauyin yanayi da illolinsa, wata kungiya, da hadin gwiwar jihohin arewa maso yammacin Najeriya da sauran masu ruwa da tsaki, sun hadu a birnin kano, don neman mafita ta bai daya.

Batun daukar matakai na bai daya wajen magance matsalolin kwararowar hamada da kalubalen muhalli da kiwon lafiya sakamakon sauyin yanayi na cikin kudirorin da aka cimma a karshen taron kwamishinonin muhalli da sauyin yanayi na jihohin arewa maso yammacin Najeriya wanda ya wakana a Kano.

Baya ga kwamishinonin kula da al’amuran muhalli da sauyin yanayi daga jihohi 7 na shiyyar arewa maso yamma, taron, wanda Kungiyar raya muhalli ta surge Africa ta shirya, ya kunshi shugabannin kwamitocin majalisun dokoki na wadannan jihohi masu kula da wannan fanni da sauran masu ruwa da tsaki.

Taro Kan Dumamar Yanayi
Taro Kan Dumamar Yanayi

Madam Nasreen Al-Amin daraktar kungiyar surge Africa tace “Wannan zance da a ke yi akan sauyin yanayi da kwararowar Hamada muna so a ce ya wuce kungiyoyin da ba na gamnati ba ne kawai suke magana akai, muna so a kawo wakilan gwamnati, da sune suke yin doka kuma suke aiwatar da ita”.

A cewar Mahmud Muhammad Abdullahi, guda cikin mahalarta taron kuma kwamishinan raya muhalli na jihar Zamfara, kalubalen tsaro da jihar ke fama dashi baya rasa alaka da sauyin yanayi da barazanar kwararowar hamada.

Bakin mahalarta taron dai ya zo wuri guda wajen ganin cewa, ya kamata wadannan jihohi guda 7 na arewa maso yammacin Najeriya su samar da manufa guda ta yakar kalubalen da sauyin yanayi ya zo dashi duk kuwa da ‘yan banbance-banbancen da ba’a rasa ba a tsakanin su.

Dr Nura Ibrahim Kazaure shine kwamishinan Muhalli na jihar Jigawa, “Ya kamata ace ko Kano tana yin wani ab una hana sare-saren bishiya ya zama cewa, Jigawa da Kaduna da sauran jihohi sunayi, domin tsarin ya tafi bai daya”.

Kafin cimma wannan manufa, majalisun dokokin jihohin 7 nada gagarumar rawar takawa. Hon Aminu Gidado shugaban kwamitin kula da harkokin muhalli da sauyin yanayi a majalisar dokoki ta jihar Sokoto ya fayyace hanyar da zasu bi, “Ta hanyar yarda ko amincewa da kasafin daya shafi ayyuka raya muhalli da kuma magance matsalolin da sauyin yanayi kan zuwa da su a kowane lokaci”.

Dama dai manzarta sun dade suna bayyana alfanun samar da tsare tsare na bai daya a tsakanin gwamnatocin arewa domin mangance kalubalen da yankin ke fuskanta a fannoni daban daban.

Saurarin rahoton Mahmud Ibrahim Kwari:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:25 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG