Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Senata Nyako Ya Shawarci Gwamna Bindowo.....


Yola, Adamawa state, Nigeria
Yola, Adamawa state, Nigeria

Senata Nyako yace yana addu'a Allah Ya baiwa Bindowo sa'ar yiwa talakawa aiki.

Shin da Senata Abdulazeez Nyako ne Gwamna Bindow Umaru Jibirlla da mukarrabansa suke yi ne , domin kwanakin baya Gwamnan ya fito yana zargin cewa wasu 'yan siyasar Adamawa wadanda suka tare a Abuja suna neman ya basu kudi, wanda yace ba zai yi hakan ba.

A karshen mako ne Senata Abdulaziz Nyako yace burinsa shine ganin Gwamna Bindow ya sami nasarar yiwa talkawan jihar Adamawa aiki, inda ya kmata ya fi maida hankali kenan, maimakon bata lokaci yana ta surutai.

A makonnin nan d a suka wuce Gwamna Bindow ya fito a kafofin yada labarai yana cewa shi bashi da uban daki. Kuma masu neman ganin wai sai ya rabu da tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubkar, sunyi a banza, domin Atiku da tsohon Gwamna Nyako duka iyayensa ne.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:01 0:00

XS
SM
MD
LG