Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

SERAP Ta Nemi Gwamnati Ta Janye Sunayen ‘Yan PDP Da Suka Saci Kudin Najeriya


Wasu kudade da aka kama a Legas.

Kungiyar da ke rajin yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya SERAP ta nemi gwamnatin tarayya ta janye jerin sunayen mutane shida da aka ce sune suka wawure dukiyar kasar.

A wani sako da ta aikowa Muryar Amurka kungiya SERAP ta nemi gwamnatin tarayya da ta gaggauta janye sunayen wasu ‘yan tsirarun PDP da ministan labaran kasar Alhaji Lai Mohammed ke cewa sune suka handame dukiyar kasa.

Maimakon haka, kungiyar ta nemi gwamnatin ta fito da cikakken sunayen duk wadanda ke da hannu wajen wawure dukiyar ‘yan Najeriya.

Da yake mayar da martani kan batun cewa jam’iyyar PDP ta dawo da kudaden da ake zargin ta sata, tsohon gwamnan jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido, ya yi zargin cewa kudin da aka sata shi ne aka yi amfani da su wajen kamfen din shugaba Buhari a shekarar 2015.

A cewar Sule Lamido, wasu ‘yan PDP ne suka dauki kudaden da suka sata suka yi amfani da su wajen zaben shugaba Mohammadu Buhari, wanda hakan ke nuna cewa "barayin ‘yan PDP" ne suka kafa wannan gwamnatin.

Wani na hannun damar shugaba Buhari kuma tsohon gwamnan jihar Yobe, Alhaji Aliyu Saleh Bagare, ya ce bai yarda da wanan kalamai da Sule Lamido ya yi ba.

Bagare ya jaddada cewa ‘yan jam’iyyar PDP ba abin da suka yi a lokacinsu sai wawure kudaden kasar.

Domin karin bayani saurari rahotan Hassan Maina Kaina.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:12 0:00

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG