Accessibility links

Shafukan zumuntar yanar gizo da gwamnatin Najeriya


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

Sau tari shafukan zumuntar yanar gizo hanya ce da jama’a ke yada labarai game da gwamnatin Najeriya ta Muhammadu Buhari. Sai dai sau da yawa wasu labaran na zama gaskiya wasu kuma sabanin hakan.

Sanin kowane kafafen shafukan zumuntar yanar gizo suna taka muhimmiyar rawa wajen yada labaran gaskiya ko sabanin haka. Wace irin rawa suke takawa a kasar don samar da labarai ga jama’a.

Wadannan kafafe suna daga cikin wadanda a yanzu suke bada bayanai daban-daban a game da gwamnatin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. Masana yada labarai na ganin dole sai gwamnatin ta fara bada bayananta don su tsira.

Muryar Amurka ta nemi jin ko menene mafita game da lamarin ta hanyar tuntubar wani dan jarida Zubair Idris Abdulra’uf na gidan radiyon Muryar Najeriya da ke Legos.

XS
SM
MD
LG