Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Buhari Ya Kaddamar da Majalisar Tattalin Arzikin Najeriya


Shugaba Muhammadu Buhari

Yau shugaba Muhammad Buhari ya kaddamar da majalisar tattalin arzikin kasar a karkashin shugabancin mataimakinsa Farfasa Osinbajo

Shugaba kasa Muhammad Buhari ya bukaci gwamnoni su tabbatar cewa sun dauk duk wani mataki da ya kamata domin biyan albashin ma'aikatansu nan take ba tare da bata wani lokaci ba.

Ya kira gwamnonin su tabbatar sun rike amana da kwatanta gaskiya a wurin mulki domin tabbatar da an yaki cin hanci da karbar rashawa wadanda yanzu suka yiwa kasar Najeriya katutu.

Shugaban kasa ya yi alwashin farfado da tattalin arzikin kasa da kuma tabbatar da cewa ya toshe duk wata hanya ko kafar da ake wawure dukiyoyin jama'a ko kuma yin almubazaranci tare da baiwa gwamnonin karfin gwiwar cewa kowannensu ya kamata ya duba hanyoyin da zai samu kudin shiga a cikin jihohinsu ba tare da ciga da dogara akan asusun gwamnatin tarayya dari bisa dari ba.

Gwamnan Zamfara Yari yayi karin haske akan taron.

Ga rahoton Umar Faruk Musa da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:21 0:00
Shiga Kai Tsaye

Bidiyo

Ko Kun San Irin Makaman Da Sojoji Ke Amfani Da Su Wajen Yaki Da 'Yan Bindiga A Jihar Zamfara?
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:31 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG