Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shagunan 'Yan kasuwa Da Dama Sun Kone Bayan Faduwar Tankar Mai Yola


Lokacin da wutar ke ci (Hoto: Channels TV)
Lokacin da wutar ke ci (Hoto: Channels TV)

Tankar man ta fadi ne yayin da direbanta ke kokain shiga shataletalen da ake kira Maidoki a birnin Yola da ke jihar Adamawa a arewa maso gabashin Najeriya.

Akalla shagunan kasuwanci 30 ne rahotanni suka ce sun kone a Yola, babban birnin jihar Adamawa da arewa maso gabashin Najeriya.

Lamarin ya faru ne bayan da wata motar tanka dauke da man fetur ta fadi ta kama da wuta.

Bayanai sun yi nuni da cewa tankar ta fadi ne a daidai shataletalen da ake kira Maidoki.

Gidan talabijin na Channels ya ruwaito cewa tankar motar ya rabu da kan motar a lokacin da ta fadi yayin da direban ke kokarin ya sha kwanar shataletalen.

Rahotanni sun ce man da ke cikin tankar ya kwarara a kwalbitin da ke yankin sannan motar ta kama da wuta.

Hakan ya sa shagunan da ke kewaye da wurin da motar ta fadi su ma suka kama da wuta.

‘Yan kasuwa da dama sun ce sun tafka asarar dukiyoyinsu, sai dai bayanai sun yi nuni da cewa ba a yi asarar rai ba.

Wadanda suka shaida lamarin sun ce ‘yan kwana-kwana a birnin na Yola sun garzaya inda tankar ta fadi suka yi ta fafatawa da wutar wacce daga karshe suka shawo kanta da kyar.

Ba dai bakon abu ba ne a Najeriya a ga motar tankin man ta fadi inda a wasu lokuta mutane kan je kwasar ganimar mai, lamarin da ke kai ga tashin gobara.

XS
SM
MD
LG