Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shahararren Mawakin Nijar Manman Barka Ya Rasu


Alh. Manman Barka
Alh. Manman Barka

Shahararren mawakin Jamhuriyar Nijar, Alhaji Maman Barka, mai gurimi ya rasu.

Ya rasu ne a yau Laraba 21 ga watan Nuwamber a Yamai bayan da ya yi fama da rashin lafiya na wani lokaci mai tsawo.

A yammacin gobe Alhamis za a yi jana’izar mamacin wanda ya rera wakokin zamantakewa sama da 100.

Galibin wakokinsa cikin harshen Hausa yake yi, abin da ya sa wadanda suka san shi ke cewa babban rashi ne ga Jamhuriyar ta Nijar.

Marigayi Mamman Barka wanda aka fi sani da suna Barkayi, ya yi fice da wakarsa ta Maryam Mariya Maryam.

A tashin farko ya dauki kada gurimi a matsayin wani abin sha’awa inda ya kan rera waka wa mutanen da suka faranta masa rai saboda soyayya ko kauna.

Wakar da ta fiddo sunansa ita ce wace ya yi wa wata masoyiyarsa Maryam lokacin da yake matsahi, hakan ya sa aka gayyace shi taron kalankuwa din da aka shirya a shekarar 1986 a Zinder kafin daga bisani ya fiddo wasu wakokin irinsu Tankari dan Garba Gidan Haya ko wakar Aure da sauransu.

Kara samun karbuwa a wannan haraka ta gurimi ta sa Maman Barka mayar da hankali kacokan akan batutuwan da suka shafi al’adu, yayin da ya ci gaba da ba da gudunmowa akan maganar ci gaban ilimi.

Malan Moussa Garba, darektan cibiyar bayar da horo a fannin kade-kade da wake-wake CFPM TAYA da ke yamai.

Da ma daga cikin matasan da suka rungumi sana’ar waka, sun ci amfanin zamansu da Alh. Maman Barka, kamar yadda Maman Sani Mati ke cewa wanda ya canza sheka daga HIP HOP zuwa makadin gurimi.

Wani binciken da mawakin ya gudanar a garuruwan kewayen tafkin Chadi, ya ba shi damar gano wani gurimin dake kan hanyar bacewa a halin yanzu, duk kuwa da cewa shi ne kayan kidin da yafi kowane shiga ran al’unmomin wannan yankin inji wani abokinsa Mousa Kambay Garba.

Jami’i a gidan raya ala’adun kasar Nijer da ake kira CCOG Maman Barka ya rasu ne a wani lokacin da yake gab da zuwa ritaya.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG