Malamin na addinin Islama ya kira musulmai da wadanda ba musulmai ba a Najeriya da suyi koyi da zamantakewar dake tsakanin mabiya addinai daban daban a kasar Amurka domin ciyar da Najeriya gaba kamar yadda tsarin Islama ya tanada.
Inji Shaikh Awal kowa ya san matsayin Amurka da musulunci da sauran addinai. Yace akwai mutanen kirki da yawa a Amurka haka kuma akwai miyagun mutane. Yace suna da 'yanci su gina masallatai tare da walwalar gudanar da addininsu.
Yace lokacin da shugaban Amurka ya ayyana dokar hana musulmai daga wasu kasashe shigowa kasar Amurkawa suka yiwa musulmai kariya suyi sallar juma'a a duk filayen jiragen sama na manyan birane.
Yana mai cewa zamantakewar mutane ta hanyar nuna soyayya da taimako shi zai jawo hankalin mutane cikin musulunci saboda haka Annabi Muhammad (SAW) ya zauna a Mecca da Medina.
Allah ya kirkiro Najeriya da kabilu daban daban da addinai da yawa da harsuna ga kuma albarka da ya ba kasar. Saboda haka 'yan Najeriya su nemi hanyar zaman lafiya da juna domin su samu cigaban kasar baki daya.
Ga rahoton Babangida Jibrin da karin bayani.
Facebook Forum